Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : A yayin ganawar da ta gudana a daren jiya a birnin New York a babban ginin Majalisar Dinkin Duniya, Ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir Abdollahian da kuma manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya kan harkokin da suka shafi Syria Geir Pedersen, bangarorin biyu sun tattauna kan halin da ake ciki a kasar ta Syria.
Baya ga haka kuma, sun tattauna kan bangarorin da za su iya karfafa ayyukansu wajen taimaka ma kasar ta Syria, da kuma ganin an kawo karshen rikicin kasar baki daya.
Abdollahian ya soki matakain Amurka na kakaba takunkumai a kan kasar Syria da ke nufin ganin an karya kasar ko ta wane hali, kamar yadda kuma ya bayyana cewa, wadannan takunkumai sun saba wa ka’ida da doka.
Kamar yadda kuma ya bayyana cewa Majalisar Dinkin Duniya za ta iya taka muhimmiyar rawa wajen ganin an janye wadannan takunkumai a kan Syria, ko kuma karya tasirinsu.
Sannan kuma ya jaddada matsayin kasarsa tabbatacce wajen nuna cikakken goyon baya ga kasar Syria da halastacciyar gwamnatin kasar.
342/